1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Uganda

Ibrahim SaniFebruary 23, 2006

Zabe ya gudana ba tare da tashe tashen hanula ba

https://p.dw.com/p/Bu1V
Hoto: AP

A cewar rahotanni da suka iso mana da yawa daga cikin wadanda suka can can ci yin zaben basu ga sunayen su a cikin rijistar zabe ba, kana hannu daya kuma wasu sun gudanar da zaben fiye da sau daya, kamar yadda doka ta bukaci ayi.

A cewar wani mai fafutikar kare hakkin bil adama da aka sakaya sunan sa,ya tabbatar da cewa wasu daga cikin jami´an tsaro sun gallazawa yan adawa a wasu runfunan , wanda hakan ya kai basu gudanar da zaben ba.

A gaba ki daya dai bayanai sun shaidar da cewa an fuskanci yan matsaloli nan da can, musanmamma na magudi da dangogin su,to sai dai kuma zaben ya gudana ba tare da an fuskanci wani mummunan tashin hankali ba, kamar yadda ake zato a can baya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zaben na shugaban kasa daya fi zafi a tsakanin shugaba mai ci, wato Yoweri Museveni da kuma Mr Kizza Besigye, na a matsayin irin sa na farko ne da jamiyyu fiye da daya suka shiga cikin sa a tsawon shekaru 25 da suka gabata.

Shugaba Museveni, wanda yake kokarin yin tazarce a gadon mulkin kasar bayan ya shafe shekaru 20 yana mulki,wani rahoton zaben jin ra´ayoyin jama´a da aka gudanar kafin wannan zabe na yau ya nunar da cewa shine ke a kann gaba, akan abokin karawar tasa.

Jim kadan da saka ku´riar sa a kauyen su dake Rushere, shugaba Museveni ya tabbatarwa da yan jaridu cewa shine zai lashe wannan zabe da gagarumin rinjaye.

A waje daya kuma ,Mr Kizza Besigye wanda cikin murmushi ya isa runfar zabe dake gundumar su da Rukungiri,nan da nan sai kamannin sa suka canza, sakamakon iske akwatun zabe da yayi a bude.

Bayan wani dan gajeren lokaci yana musayar miyau a tsakanin sa da jami´an zaben, rahotanni sun nunar da cewa an samu damar shawo kann al´amarin.

To sai dai kuma jim kadan da kada kuri´ar tasa kafafen yada labaru sun rawaito shi yana fadin cewa babu shakka za´a iya fuskantar matsaloli irin wadannan da kuma ma wasu na daban a wasu runfunar zaben a wasu guraren.

Bayanai dai a can baya sun nunar da cewa da yawa daga cikin kasashen yamma na yabawa da irin matakan da shugaba Yoweri Museveni ke dauka na inganta rayuwar yan kasar, da cewa hakan yasa ya fita zakka a tsakanin shugabanni a nahiyar Africa.

To sai dai kuma bisa irin yadda gwamnatin sa ta aiwatar da kisisinar yin yan gyare gyare a kundin tsarin mulkin don ya samu yin tazarce a karo na uku da kuma yadda ake tuhumar Mr Kizza Besigye a kotu bisa cin amanar kasa da kuma yiwa wata mace fyade ya haifar kasashen yamman sun dawo daga rakiyar sa.

Da yawa dai daga cikin masu nazarin harkokin siyasa a kasar, musanmamma daga bangaren yan adawa na ganin cewa ci gaba da mulkin shugaba Museveni ba zai zamewa kasar Alhairi ba musanmamma ta fannin dorewar mulkin dimokradiyya.