1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZABEN SHUGABAN KASA DANA YAN MAJALISA A MOZAMBIQUE.

December 1, 2004
https://p.dw.com/p/BveN
Jamiun Zabe da masu kada kuria.
Jamiun Zabe da masu kada kuria.Hoto: AP

A yau ne alummar kasar Mozambique ke kada kuriunsu na zaben shugaban kasa domin maye gurbin shugaba Joaquim Chissano,wanda yayi shekaru 18 yana kann wannan karaga,tare da yan majalisar dokokin kasar.

Gwamnatin kasar ta Mozambique dai tayi amfani da jirage masu kirar saukar ungulu da jiragen ruwa na kwale kwale wajen rarraba akwatunan zabe da katuna zuwa yankunann karkara domin samun nasaran gudanar da zaben na yau.

Hamshakin dan kasuwa Armando Guebuza mai shekaru 60 da haihuwa kuma dan jammiyar Frelimo ta shugaba Chissano,na kalubalantar dan takara Afonso Dhlakama mai shekaru 51 na jammiyar tsohuwar kungiyar adawar kasar,Renamo.Kana akwai wasu yan takaran kujeran shugabancin kasa guda uku daga wasu jammiyyu kanannan kasar,ayayinda a yau din ne kuma zaa kada kuriun zaben sabbin yan majalisar dokokin Mozambique din.

Bayan ya kada kuriarsa ta karshe amatsayinsa na shugaban kasa,Chissano ya bayyana cewa jiragen kwale kwale sunyi jigilar kayyaki da akwatunan zabe zuwa kauyukan da motoci bazasu iya zuwa ba saboda munin hanya.Har yanzu Mozambique na fuskan tar matsalolin lalatattun hanya da rusassun gada ,sakamakon ambaliyar ruwa da kasar da fuskanta shekaru 2 da suka gabata,wanda kuma ke haifar da matsaloli wajen sadarwa zuwa wasu yankuna.

Masu gani da ido sun bayyana cewa dumbin alummar kasar na cikin jerin layi na kada kuriun duk da ruwan sama dake kwararowa tun daga wayewan garin yau a gunduwar Manhica.amakon daya gabata nedai mutane biyu suka rasa rayukansu ,kana asibitin garin ya rushe sakamakon ambaliyan ruwa.

Masu gani da ido na kasashen ketare dai sun bayyana cewa ya zuwa yanzu zaben na tafiya cikin lumana da kwanciyar hankali,a duk yankuna da suka ziyarta ,kodayake jammiyar adawa ta renamo koka da matsalolin yin registan masu zabe a gunduwar Tete da Maputo.

Yan takara Guebuza da Dhlakama sun kada nasu kuriun ne a birnin Maputo,inda kowannensu ke fatan samun nasara,musamman Dhlakama,wanda ya koka da irin magudi da aka tabka a zaben shekarun 1994 dana 1999.Sai dai ya fadawa manema labaru cewa cewa bisa dukkan alamu wannan karon akwai alamun gaskiya da adalci.Ya jaddada cewa shekaru 30 kenan da jammiyar Frelimo ke mulkin Mozanbique,kuma lokaci yayi da zaa samau sauyi.

To sai dai manazarta na ganin cewa koda wanne dan takara yayi nasara bazai sauya alkiblar harkokin cigaba ba wannan kasa ba,wadda ke zama wurin da Bankin duniya ta kaddamar da babban shirinta na sake ginin ta,bayan yakin basasa lokaci mai tsawo,da aka kawo karshensa a shekara ta 1992.

Duk dacewa an samu ingantuwan tattalin arziki a shekaru 10 da suka gabata da wajen kashi 10 cikin 100,har yanzu fiye da rabin alummar Mozambique da yawansu yakai million 18,na rayuwa cikin kangin talauci,kana kashi 50 daga cikin su na fuskantar rashin aiki.

Koda yake yana daman sake tsayawa takaran shugabancin kasar,Chissano dake kann karaga a yanzu yace zai sauka domin bawa Democradiyya fili.Bugu da kari,ayau din ne kuma zaa zabi yan majalisar dokoki 250,wanda ke zama na ukun irinsa a Mozambique data kasance a karkashin mulkin mallakan Portugal.kimanin mutane million 9.1 sukayi rigistan kada kurounsu a cibiyoyin zabe 12,800 da aka tanadar.

Zainab A Mohammed.