1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Shugaban Kasar Jamus

May 18, 2004

A ranar lahadi mai zuwa 23 ga watan mayu majalisar tarayya da ta kunshi wakilan majalisar dokoki ta Bundestag da na majalisun jihohin tarayya 16 zata kada kuri'a domin zaben sabon shugaban kasar Jamus da zai maye gurbin Johannes Rau mai barin gado

https://p.dw.com/p/BvjU
Shugaban kasar Jamus mai barin gado Johannes Rau
Shugaban kasar Jamus mai barin gado Johannes RauHoto: dpa

Bayan kowadanne shekaru biyar-biyar wakilan majalisar tarayya su kimanin dubu daya da dari biyu da shida su kan hallara a zauren majalisar dokoki ta Bundestag domin zaben shugaban kasar Jamus. Ita majalisar ta tarayya ta hada ne da wakilan majalisar dokoki ta Bundestag da kuma na majalisun jihohin tarayya guda 16 da ake da su a nan kasar. Domin bikin nadin sabon shugaban ya kara armashi jam’iyyun siyasa kan gayyaci manyan baki dake taya murna. Akan gayyaci gaggan ‚yan wasan motsa jiki da shahararrun ‚yan wasan kwaikwayo da mawaka da ‚yan kasuwa da makamantansu. A wannan karon jam’iyyun FDP da ‚Yan Christian Union su ne ke da rinjaye na 18 na jumullar kuri’un tare da wakilai 622. Sai dai kuma wannan rinjaye bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da wakilai 461 na jam’iyyar SPD da 89 na the Greens da kuma 31 daga jam’iyyar PDS da tafi angizo a gabacin Jamus. Za a fara kada kuri’ar ne a daidai karfe 12 na ranar 23 ga watan mayu, kuma idan ba a samu dan takarar da ya samu gagarumin rinjaye ba sai a shiga mataki na biyu, sai kuma mataki na uku, inda za a amince da dan takarar da ya samu rinjaye a’ala, sannan a gabatar da bikin rantsar da shi a ranar daya ga watan yuli. Bisa sabanin yadda lamarin yake a kasashen Faransa da Amurka ko Rasha, a nan Jamus shugaban kasa ba ya da cikakken ikon zartaswa. An ba shi wani matsayi ne na uban kasa dake sauraron kararrakin dukkan ‚ya’yansa ya kuma yi bakin kokarinsa wajen dinke dukkan barakar da ka samu tsakaninsu ba tare da nuna son kai ba. Yawa-yawanci wadannan shuagabannin kan yi tasiri a al’amuran siyasa da zamantakewar jama’a ne ta kan jawaban da suke gabatarwa a bainar jama’a. Shugaban dai shi ne ke wakiltar Jamus a cikin gida da ketare, kuma shi ne ke tabbatar da shugaban gwamnati ko kuma korarsa daga bakin aikinsa, kazalika da sauran jami’an gwamnati da alkalin-alkalai da sauran mahukunta na tarayya. A baya ga haka yana da ikon rushe majalisar dokoki ta Bundestag da bita tare da sa hannu akan duk wata sabuwar dokar da za a gabatar. Shi ne kuma ke ba da lambobin yabo na kasa ga wadanda suka cancanta tare da yi wa fursinoni afuwa. A huldodi na jama’a kuma shugaban kasar ne ke rike da shugabanci na alfarma ga kungiyoyi dabam-dabam ya kuma aike da sakon taya murna ga duk wani dan kasa da ya samu shekaru dari da haifuwa. A manufofi na ketare kuwa, shugaban kasar Jamus ne ke wakiltar kasar bisa tsarin yarjeniyoyi na kasa da kasa kuma as sakamakon haka ziyararsa ga kasashen waje ta zama wani bangare na manufofin ketare na kasar bisa manufar karfafa dangantaku na siyasa.