1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Shugaban Kasar Jamus

May 7, 2004

A ranar 23 ga watan mayu ne majalisar wakilai ta Jamus zata zabi shugaban kasa a tsakanin 'yan takara guda biyu da suka hada da Horst Köhler tsofon darektan asusun IMF a karkashin tutar'yan Christian Union da Gestine Schwan 'yar takarar jam'iyyun SPD da The Greens

https://p.dw.com/p/Bvjp
Horst Köhler dan takarar Christian Union da ake sa ran zai cinye zaben shugaban kasar Jamus a ranar 23 ga watan mayu
Horst Köhler dan takarar Christian Union da ake sa ran zai cinye zaben shugaban kasar Jamus a ranar 23 ga watan mayuHoto: AP

A bisa al’ada dai ba a fuskantar wata ba zata a duk lokacin da aka zo zaben shugaban kasar Jamus. Kuma kamar yadda aka saba kowane daka cikin ‚yan takarar da jam’iyyun siyasar suka nada na cikin cikakkiyar damara domin tsayawa gaban wakilan majalisar ta tarayya a daidai ranar 23 ga watan mayu. Amma fa a hakika zai zama abin mamaki idan dan takarar jam’iyyun CDU/CSU da FDP kuma tsofon darektan asusun IMF Horst Köhler ya sha kayi a hannun Gestine Schwan ‚yar takarar jam’iyyun hadin guiwa na SPD da The Greens. Abubuwa masu jirkitaswa da dama suka faru kafin nadin wadannan ‚yan takara guda biyu domin neman wannan mukami na alfarma. Saboda a karo na farko lamarin ya dauki wani fasali mai kama da yakin neman zabe. A karkashin wannan yanayi na yakin neman zabe kowane daga cikin ‚yan takarar sai da ya rika shiga mukabala ta gidajen telebijin da hadar da tarurruka da manema labarai domin bayyana matsayinsa. Kazalika sun yi mukabala da daidaikun wakilan majalisar tarayya, wadanda suka hada da wakilan majalisar dokoki ta Bundestag da kuma majalisun jihohin tarayya. An ba wa lamarin wata suffa ta gasa alhali kuwa kowa ya san inda makwancin mafiya rinjaye yake, amma duk da haka Köhler yayi aiki da shawarar mashawartansa na kin mukabala keke-da-keke da abokiyar takararsa, wacce Allah Yayi mata fasahar iya magana.

Sai dai kuma wani sabon abu a game da zaben shugaban kasar, wanda kuma ga alamu yake da nasaba da mawuyacin hali na siyasa da ake ciki a nan Jamus, shi ne kasancewar ‚yan takarar ba su da wata nasaba da jam’iyyun siyasar da suka tsayar da su kuma ba su taba tunanin rike mukamin shugaban kasa ba. wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya dukkansu biyu ke samun goyan baya daga kafofin yada labarai, lamarin da ya ba wa harkar nadin shugaban kasar wani sabon jini, saboda sha’awar fadin albarkacin bakinsu da suke yi. Wani abin mamaki ma shi ne yadda dukkan ‚yan takarar guda biyu, maganar rashin yarda da ‚yan siyasa dake dada yaduwa a zukatan jama’a yake ci musu tuwo a kwarya. Galibi ma idan mutum yayi bitar bayanai da suke bayarwa zai tarar sun yi daura da ainifin alkiblar da jam’iuyyun da suka tsayar da su takarar suka fuskanta. Maganganu da ‚yan takarar ke yi tsakani da Allah ba tare da wata rufa-rufa ba abu ne da ya kara musu farin jini tsakanin jama’a, duk kuwa da bacin rai da wasu jami’an siyasar wadannan jam’iyyu kan nunar. Masu iya magana dai sun ce rana ba ta karya sai dai uwar ‚ya ta ji kunya. A saboda haka sai mu zura ido mu ga yadda zata kaya a ranar 23 ga wannan wata na mayu lokacin da majalisar wakilai ta tarayya zata zabi daya daga cikin 'yan takarar guda biyu akan mukamin shugaban kasar Jamus.