1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasar Liberia a yau talata

November 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvLz

An fara kada kuri´a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Liberia, inda ake takara tsakanin tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar kasar George Weah da kuma tsohuwar jami´ar bankin Duniya Ellen Johnson Sirleaf. Kowannen su na fafutukar samun rinjaye a zaben na shugaban wannan kasa dake yankin Afirka Ta Yamma. Mutane fiye da miliyan daya da dubu dari uku daukacinsu matasa ke kada kuri´ar ta yau a mazabu kimanin dubu 3 da aka tanadar a fadin kasar. Sakataren janar na MDD Kofi Annan ya bukaci al´umar kasar su kada kuri´ar lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ba. Kana kuma su amince da sakamakon zaben. Ana fatan samun cikakken sakamakon zaben cikin makwanni biyu. A zagaye na farko na zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Oktoba babu wanda ya sami adadin kuri´un da ake bukata ta samun rinjaye.