1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben yan majalisar dokoki a Afganista

Zainab A MohammadSeptember 13, 2005

Ranar Lahadi mai zuwa ne ake saran gudanar da zaben yan majalisa a Afganistan

https://p.dw.com/p/BvZg
Hoto: AP

Shugaba Hamid Kharzai na Afganistan yayi kira ga kasashen duniya da kada suyi watsi da kasarsa dake fama da rikice rikice,bayan zaben yan majalisar dokoki a wannan mako da muke ciki.

Shugaba Kharzai yace kasashen duniya,wadanda suka zuba biliyoyin daloli a Afganistan tun bayan kifar da gwamnatin yan Taliban a shekarata 2001 ,kawo yanzu sunada muhimmiyar rawa da zasu taka wajen samarda da ingantaccen tsaro da sake ginin kasar.

Yace fatansu shine kada duniya ta juya musu baya,da zarar an kammala zaben kasar ,kann cewar yanzu Afganistan nakan kafafunta,domin injishi har yanzu kasar bata da madogara face tallafi da goyon baya da take samu daga kasashen wake.

Shugaban Afganistan wanda yayi wadannan kalaman ayayinda yake jawabi wa wakilai 30,dake jagorantar kabilu da sarakuna da malaman addini a garin Herat dake yammacin kasar,yakara dayin kira da akara agazawa musu wajen sake farfado da masanaantun kasar.

Kharzai yace akwai bukatar kasashe su cigaba ta basu tallafi daya suka dace domin samun sukunin sake farfado da sashin yansanda,da makarantu da soji da kuma sashin sharia.

Bugu da kari shugaban na Afganistan yayi kira ga tsoffin mayakan taliban da suka tsere zuwa pakistan dake makwabtaka ,dasu dawo gida domin gudanar da yancinsu na yan kasa a wannan zabe da zai gudana.

Yace akwai bukatar masu bada gudunmowa su tabbatar dacewa bayan gudanar da zaben yan majalisar dokoki,sun kuma raka ta domin ganin cewa ta samu zama da gindinta.

Zaben yan majalisar dazai gudana ranar lahadi idan mai duka ya kaimu,na mai zama karo na biyu da Afganistan zata sake hawa babban matsayi ,cikin wannan hali da take ciki na rashin inda aka dosa,dangane da batutuwan zaman lafiya a kasar.Zaben da kuma ke bin bayan na shugaban kasa daya gudana a watan Oktoban bara.

Wannan zaben dai shine zai tabbatar da kawo karshen shirin tallafawa kasar na tsawon shekaru hudu da aka zana a birnin Bonn din nan jamus,bayan da dakarun hadin gwiwa a karkashin jagorancin Amurka suka kifar da gwamnatin yan taliban a shekarata 2001,amma masu agajin na shirin sake gudanar da taro a birnin London a watan janairu,domin sake nazarin wani sabin shiri na agaji wa Afganistan.

A makon daya gabata nedai mdd ta sanar dacewa har yanzu harkokin siyasan Afganistan na bukatar ingantaccen tsaro,kuma bisa dukkan alamu akwai sauran rina a kaba,a dangane da hakane ,kasar ke bukatar tallafin kasashen duniya na lokaci mai tsawo.