1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben yan majalisun dokoki a Zimbabwe ya samu cikas

November 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvIo

Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun shaidar da cewa kashi 20 ne cikin dari na wadanda suka cancanci yin zabe a kasar suka kada kuri´un su a lokacin zaben yan majalisun dokokin kasar da aka gudanar a ranar asabar din data gabata.

Rashin fitowar alummar kasar a cewar bayanai nada nasaba da kiran da jamiyyar adawa ta MDC tayi ne na a kauracewa wannan zabe.

Da yawa dai daga cikin masu nazarin harkokin yau da kullum na ganin cewa, rashin fitowar mutane yadda yakamata a lokacin wannan zabe alamace dake nuna rashin amincewa da gwamnatin kasar karkashin shugaba Robert Mugabe.

Rahotanni dai daga kasar na nuni da cewa kusan kashi tamanin cikin dari na alummar kasar na cikin hali ne na fatara, kana a hannu daya kuma ga matsaloli na rashin aikin yi.