1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabukan shugaba da na ´yan majalisar dokokin tsibirin Zanzibar

October 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvNJ

A yau ake gudanar da zabukan shugaba da na ´yan majalisar dokokin tsibirin Zanzibar na kasar Tanzaniya. Rahotanni sun ce an yi arangama tsakanin magoya bayan ´yan adawa da masu zabe da suka yi zargin cewa jam´iyar dake jan ragamar mulki ta kawo su don su kada kuri´a. An tura sojoji zuwa mazabu biyu dake garin Stone Town mai dadadden tarihi don kwantar da tarzoma bayan wannan arangama. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya rawaito cewa sojoji sun yi harbi cikin iska tare da amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu ba hamata iska. An girke ´yan sanda kimanin dubu 35 don hana barkewar wani mummunan tashin hankali irin wanda aka fuskanta lokacin zaben da ya gudana a shekara ta 2000. A wannan karon dai ana takara tsakanin shugaba Amani Karume da babban abokin hamaiya Seif Sharif Hamad. Ana gudanar da zaben a Zanzibar gabanin na Tanzaniya wanda aka dage saboda mutuwar wani dan takara na ´yan adawa sakamakon rashin lafiya.