1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na biyu a zaben ´yan majalisar dokokin Masar

November 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvKI
A daidai lokacin da aka fara zagaye na biyu daga cikin uku na zaben ´yan majalisar dokokin Masar, ´yan sanda sun kame mutane 200 dukkansu magoya bayan kungiyar ´yan adawa ta ´yan´uwa musulmi. Jami´an tsaro sun ce tun a ranar juma´a aka fara kame kamen. A zagaye na farko na zaben wanda ya gudana a ranar 9 ga wannan wata na nuwamba, kungiyar ta ´yan´uwa musulmi wadda a hukumance an haramta ta, amma duk da haka ana hakuri da wanzuwarta, ta kasance ´yar adawa da tafi taka rawar gani a zaben. Kungiyar dai tana da yawan magoya baya musamman a tsakanin talakawan kasar saboda ayyukan alheri da take yi a unguwannin marasa galihu. A ranar 7 ga watan desamba za´a gudanar da zagaye na uku kuma na karshe. Jam´iyar shugaba Hosni Mubarak aka yi hasashe zata lashe zaben.