1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na biyu na zaɓen ´yan majalisar dokokin janhuriyar Kongo

August 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuEh
A yau ake gudanar da zagaye na biyu na zaben ´yan majalisar dokokin janhuriyar Kongo, inda ake takarar kujeru 84 a wannan kasa makwabciyar JDK. A zagayen farko na zaben wanday a gudana a ranar 24 ga watan yuni, jam´iyar Labour ta shugaban kasa Dennis Sassou Nguesso ta lashe kujeru 50 daga cikin 53 da aka yi takara kan su. To sai dai an tabka magudi a zaben. Ko da yake kasar ta janhuriyar Kongo mai yawan al´uma miliyan 4 ta na da arzikin man fetir amma daukacin mutanen ta na fama da mummunan talauci.