1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman Juyayi a Berlin dangane da mutanen da suka rasu a tsautsayin tsunami

January 10, 2005

A jiya lahadi aka gabatar da zaman juyayin mutanen da bala'in tsunami ya rutsa da su a kudancin Asiya, a babbar mujami'ar Berlin

https://p.dw.com/p/Bvdj
Zaman juyayi a babbar mujami'ar Berlin
Zaman juyayi a babbar mujami'ar BerlinHoto: AP

Daga cikin wadanda suka halarci zaman juyayin a babbar mujami’ar Berlin har da shugaban kasa Horst Köhler da shugaban gwamnati Gerhard schröder da wasu daga ‚ya’yan majalisar ministoci da jami’an hamayya, sai kuma gwamnonin jihohin Jamus da kuma jami’an diplomasiyyar kasashen ketare. Shugaban majalisar limaman katolika ta Jamus Cardinal Karl Lehmann da takwaransa na mujami’ar Evangelikan Bishop Wolfgang Huber sun gabatar da gashe-gaishensu na ta’aziyya ga ‚yan-uwa da dangin dukkan wadanda tsautsayin ya rutsa da su a yankin kudancin Asiya. Kazalika dukkansu biyu sun yaba da kwararan matakai na taimako da Jamus ta dauka, a cikin kiftawa da Bisimillah, da kuma jami’an da suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da asalin gawawwakin da aka tuno ta yadda za a iya mika su ga danginsu a cikin mutunci. An saurara daga bakin limamin limaman ‚yan Katolika na Jamus Cardinal Karl Lehmann yana mai nuni da cewar muna da ta’aziyyarmu zuwa ga dukkan wadanda lamarin ya shafa da kuma bakin cikin asarar danginsu da suka yi. Shi ma a nasa bangaren babban limanin mujami'ar Evangelikan Bishop Wolfgang Huber ya gabatar da tasa gaisuwar ta ta’aziyya a cikin hudubar da ya bayar, wacce aka nunar kai tsaye ta gidajen telebijin. Bishop Huber yayi nuni da kakkarfar azamar da mutane suka nunar wajen gabatar da taimakon da ba a taba ganin irin shigensa ba a cikin tarihin dan adam na baya-bayan nan daidai da wannan bala’in da ya rutsa da kasashe 12 a lokaci guda. Wannan bala’i ya dada kusantar da sassan duniya da juna, saboda kusan ya shafi kowa da kowa. Wannan tamkar wata dama ce ga dan-Adam ya canza salon tunani, ya kuma mayar da hankali ga wani tsarin zamantakewa akan turba ta adalci da taimakon juna, in ji Cardinal Karl Lehmann, wanda ya kara da cewar ba shakka hutunan barnar da igiyar ruwan tayi da aka rika nunawa ta akwatunan telebijin abu ne da zai tunasar da da yawa daga cikin Jamusawa halin da suka kasance a ciki a bayan yakin duniya na biyu. Jim kadan bayan kammala zaman juyayin shugaban gwamnati Gerhard Schröder, a cikin wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, ya ba da sanarwa a game da wata manufar siyasa bai daya da za a dauka wajen hada kan taimakon da ake bayarwa ga kasashen da lamarin ya shafa. Kazalika yayi kira ga Jamusawa dake sha’awar yawon bude ido da cewar ka da su yarda wannan bala’in ya tsoratar da su, su daina kai ziyarar shakatawa a kasashen kudancin Asiya, domin yin haka tamkar wani sabon bala’i ne dangane da makomar kasashen yankin, wadanda suka dogara kacokam akan harkokin yawon bude ido domin samun kudaden shiga.