1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman Kotu a Iraqi

Ibrahim SAniFebruary 13, 2006

An koma ci gaba da sauraron shari´ar Saddam Hussain da mukarraban sa guda bakwai a Bagadaza

https://p.dw.com/p/Bu1m
Hoto: DW

Kotun dai ta gudanar da zaman nata ne na yau tare da halartar Saddam Hussain, sabanin alkawarin da yayi a can baya cewa ba zai sake halartar zaman kotun ba.

To sai dai wakilin kamfanin dillancin labaru na Reuters ya rawaito Saddam Hussain na fadin cewa tursasa masa akayi ya halarci zaman wannan kotu, amma ba a son ran sa ba.

Jim kadan da isar su cikin kotun, Saddam Hussain tare da dan uwan sa Barzan Al Tikriti, sun kalubalanci kotun da cewa bata da hurumin gudanar da wannan shari´a , domin a cewar su an kafa tane a karkashin jagorancin Sojin mamaye na Amurka.

Saddam Hussain, wanda har yanzu ke kann bakansa na cewa shine shugaban kasar ta Iraqi, ya kira kotun da cewa wani dandali ne na wasa kawai, amma ba kotu ba.

Bugu da kari tsohon shugaban kasar ta Iraqi, yaki amincewa kotun ta bashi lauyoyi da zasu kare shi, bisa kauracewa zaman kotun da lauyoyin sa suka yi a tun watan daya gabata, bisa irin tsauraran matakai na son rai da suka zargi Alkalin kotun dayi.

Saddam Hussain na dan uwan nasa Barzan sun mike tsaye a cikin kotun suna kalubalantar alkalin kotun , wato Raouf Abdel Rahman, wanda jami´an gwamnatin kasar ke kallon sa a matsayin mutumin da zai dauki kwararan matakai na gaggauta yankewa Saddam Hussain da mukararraban nasa hukunci, idan an same su da laifi.

Kafin dai fara zaman kotun na yau, bayanai sun shaidar da cewa kotun ta shirya gabatar da wasu tsoffin jami´ai na gwamnatin na Saddam , wato Ahmed Khudayir da Hassan Al Obeidi, a zaman na yau domin su bayar da shaida.

Duk da kokarin da kotun tayi na kawo Ahmed Khudayir , zaman kotun na yau, tsohon jami´in leken asiri na kasashen waje a lokacin mulkin Saddam Hussain ya tabbatarwa da kotun cewa bashi da cikakken bayanin da zai bada shaida a game da batun da ake cajin tsohon shugaban na Iraqi da mutane bakwan.

Khudayir yaci gaba da cewa tursasa masa akayi yazo zaman kotun domin ya bayar da shaida, shi kuma a kashin gaskiya bashi da cikakken bayanin da zai bada shaida akan abin da ake zargin tsohon shugaban kasar da mukararraban nasa bakwai.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa masu gabatar da karar a can baya sun zata cewa tsoffin jami´an gwamnatin na Saddam Hussain ka iya taimaka musu tabbatar da laifin da ake zargin tsohon shugaban kasar na Iraqi da ragowar mutane bakwan, to amma abin sai ya kasance da daukar sabon salo.

Ba a da bayan, Khudayir, da yawa daga cikin wadanda suka bayar da shaida a yau, sun yi waiwaye ne wanda hausawa kance adon tafiya a game da irin cin mutunci da gallazawa da akayiwa yayan su da yan uwan su, wanda hakan ya kai ga asarar rayukan su a lokacin mulkin na Saddam Hussain.

Bayanai dai sun nunar da cewa, a yayin da daya daga cikin shaidun ke bayar da bayani a bayan labule, sai Saddam ya katse hanzarin sa da cewa, babu kanshin gaskiya a cikin abin da yake fadi, illa kawai siyasa ce tsagwaronta.

Wannan kotun dai na zargin Saddam Hussain na mukararaban nasa da yin kisan kiyashi ga mutane 148 na garin Dujail a shekara ta 1982, bisa wani yunkuri da mutanen garin suka yi na kisan Saddam Hussain a lokacin yana shugaban kasa.

Matukar dai wannan kotu ta samu Saddam Hussain da mukararraban nasa da wannan lafi da ake zargin su da aikatawa to babu makawa hukuncin kisa ya hau kann su ta hanyar rataya.