1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman majalisar Iraƙi.

June 14, 2010

Majalisar dokokin Iraƙi ta yi zamanta na farko bayan zaɓen watan Maris.

https://p.dw.com/p/Nqhi
Zaman majalisar dokin Iraƙi na farko bayan zaɓen watan Maris.Hoto: AP

Bayan watanni uku na shiga ruɗanin siyasa, majalisar dokokin Iraƙi ta yi zamanta na farko tun bayan zaɓen da ya gudana a ƙasar da ba a tatance ba. Cikin minti 20 kacal ne aka yi wannan zama wanda a yayinsa 'yan majalisar ga baki ɗayansu suka karɓi rantsuwar kama aiki. Tun bayan zaɓen ranar bakwai ga watan Maris ne dai ake rashin wanda zai samar da yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗaka tsakanin tsohon framinista, Iyad Allawi da fraministan riƙon ƙwarya, Nuri Al-Maliki. Kuma har yanzu an kasa naɗa waɗanda za su riƙe muhimman muƙamai da suka haɗa da na shugaban majalisar dokoki. Wannan giɓi na siysa dai ya samu ne watanni biyu kafin dakarun Amirka su fara ficewa daga ƙasar ta Iraƙi. Gwamnatin Iraƙi ta ƙiyasce cewa mutane 337 suka rasa rayukansu a rikicin da ya ɓarke a watan Mayu.

Mawallafiya: Haima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu