1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

zaman makoki a Rasha

March 30, 2010

Dubban 'yan ƙasar Rasha ne suka fara zaman makoki, inda zuke nuna jimami bisa harin ta'addanci da yafaru

https://p.dw.com/p/MiHE
Jami'an tsaron RashaHoto: AP

A yaune ake zaman makoki a ƙasar Rasha, domin tunawa da mutane 38 waɗanda wani harin ta'addanci ya hallaka a jiya. Dubban 'yan ƙasarne sukayi ta ajiye faranni a wurin da hatsarin yafaru, wato tashar jiragen ƙasa na Lubyanka. A lin da ake ciki dai jami'an tsaro sun shiga binciken waɗanda ke da hannu a wannan harin. Ministan harkokin wajen ƙasar Sargei Lavrov, ya shaidawa taron ƙasashen G8 da ke gudana a ƙasar Kanada cewa, ba za su fidda tsammanin hannun wassu daga waje ba, inda yake nuna yatsa ga 'yan ta'adda dake kan iyakar Pakistan da Afganistan. Jami'an tsaron Rasha dai sun ɗorawa 'yan tawayen arewacin Caucasus, waɗanda suka haɗa da Chechenya da kuma na Ingushetiya. Da yake ajiye fure a tashar jiragen ƙasa dake Lubyanka in hatsarin ya faru, shugaba Dmitri Medvedev yace sai sun tsaƙulo wanɗanda suka kai harin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi