1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman makoki a Ukrain da Rasha

August 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bulq

A yau alúmar ƙasar Ukrain suka shiga zaman makoki domin nuna alhini ga mutanen da suka rasu a haɗarin jirgin saman Rashan wanda ya fadi a gabashin ƙasar ta Ukrain ɗauke da fasinjoji 170. Wasu daga cikin dangin mamatan za su tashi zuwa wurin da haɗarin ya auku domin gano gawarwakin yan uwan su. Maáikatan ceto na ta lalube domin gano akwatun bayanai na jirgin. Wannan shi ne haɗari na biyu wanda aka yi hasarar rayukan jamaá masu yawa a cikin sa, a haɗarin jiragen saman Rasha cikin watanni biyu. Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya kebe ranar Alhamis din nan a matsayin ranar makoki a faɗin ƙasar baki ɗaya.