1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman zullumi a Cote d'Ivoire

November 26, 2010

Rigingimu gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a Cote d'Ivoire

https://p.dw.com/p/QJdT
Shugaba mai ci a Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo wajen yaƙin neman zaɓeHoto: picture alliance/PANAPRESS/MAXPPP

A wannan makon jaridun na Jamus sun mayar da hankali akan batutuwa da dama na nahiyarmu ta Afirka. Amma da farko bari mu fara da ƙasar Cote d'Ivoire inda a rahotonta jaridar Die Tageszeitung ta fara da cewa an shiga zaman zullumi a gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar ta Cote d'Ivoire. Jaridar ta ce gabanin zaɓen a wannan Lahadin an yi ta samu tashe tashen hankula tsakanin magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo da na mai ƙalubalantarsa Alassane Watara. Akan haka jaridar ta rawaito hafsan hafsoshin sojin ƙasar Janar Philippe Mangou na cewa za a ɗauki matakin ba sani ba sabo akan waɗanda ya kira masu ta da zaune tsaye dake son jefa ƙasar a cikin mummunan halin da ta taɓa samun kanta a ciki.

Italien Libyen Muammar Gaddafi bei Silvio Berlusconi in Rom
Shugaban Libya Moammar Gadhafi, tsaye a hagu da Firaministan Italiya Silvio Berlusconi, a damaHoto: AP

Gaddafi zai karɓi baƙoncin taron ƙoli, wannan shine taken rahoton jaridar Neues Deutschland tana mai mayar da hankali kan taron karo na uku tsakanin shugabannin Afirka da na Tarayyar Turai da zai gudan a ranakun 29 da 30 ga watannan a birnin Tripolis na ƙasar Libya. Ta ce a da Muammar Ghaddafi ya kasance ɗan tsagera amma yanzu shi ne babban abokin ɗasawar EU musamman a batun 'yan gudun hijira. Jaridar ta ce tun bayan taron ƙolin na farko tsakanin ɓangarorin biyu a birnin Lisbon, batun ƙawancen tattalin arziki, zaman lafiya da kuma tsaro ke kan gaba. EU dai na tallafawa Libya wajen daƙile kwararowar baƙin haure waɗanda ke bi ta ƙasar suna shigowa ƙasashen Turai.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Kongo ya yi watsi da zargin da ake masa, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ne mai nuni da shari'ar da akewa Jean-Pierre Bemba a kotun ƙasa da ƙasa dake birnin The Hague. Jaridar ta ce Bemba wanda ya sha kaye a zaɓen shugaban Kongo a shekarar 2007 kuma ya tsere daga ƙasar bayan wannan zaɓe, ya musanta zargin da kotun ke masa cewa a matsayinsa na jagoran ƙungiyar 'yan tawayen MLC, shi ke da alhakin ta'asar da sojojinsa suka aikata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tsakanin shekarun 2002 da 2003, inda suka aikata kisan ƙare dangi, yiwa mata fyaɗe na gama gari da kwasar ganima.

Jean-Pierre Bemba Internationaler Strafgerichtshof
Jean-Pierre Bemba zaune a kotu a bayan ɗaya daga cikin lauyoyinsaHoto: dpa

A nan Jamus ma a wannan makon aka gurfanar da wasu 'yan fashin jirgin ruwa na ƙasar Somaliya a gaban wata kotu ta birnin Hamburg. Jaridar Die Welt wadda ta mayar da hankalin kan shari'a cewa ta yi a karon farko cikin shekaru 400 an sake gurfanar da 'yan fashin teku a gaban kotu a Hamburg. Ta kwatanta halaiyar 'yan fashin na yanzu da na zamanin da tana mai cewa dukkansu sun kasance a ƙasashe marasa gwamnatoci ko hukumomi tsayayyu, wato kenan suna kashe mu raba ne da masu taimaka musu da makamai da sauran kayan da suke aikata wannan ɗanya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu