1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zamantakewa tsakanin al´umomin Bosniya

December 5, 2007
https://p.dw.com/p/CXYQ
'Yar BudurwaHoto: eurovision.tv

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka sahfi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Auratayya tsakanin kabilu da mabiya addinai daban daban ba wani abu ne na musamman a tsohuwar tarayyar Yugoslabiya ba. Kimanin kashi 30 cikin 100 na yawan aure gabanin yakin Bosniya an yi shi tsakanin al´umomin kabilu daban daban da mabiya addinai na wannan kasa. Aurayya tsakanin al´umomin Sabiya da Kuratiya ko Kuratiya da musulmi ko Sabiyawa da Musulmi ba bakon abu ba ne musamman a Bosniya Herzegovina wadda ta kasance abar misali na wata kyakkyawar zamantakewa tsakanin mabiya addinai da kabilu barkatai a cikin wata janhuriya guda. To sai dai tun bayan yakin Bosniya kyakyawan yanayi na nuna juriya ya canza kwarai da gaske, inda yanzu haka mutane da yawa suka fi danganta kansu da addinin su wato Musulmi da Kirista. Alkalumman MDD sun yi nuni da cewa kimanin kashi 60 cikin 100 na al´umar Bosniya-Herzegovina na adawa da auratayya tsakanin kabilu ko mabiya addinai daban daban. Wakilin DW Elif Senel ya yi tattaki zuwa birnin Sarajevo inda ya ci karo da wasu masoyan juna wadanda bambamcin addini ko na kabila ba ya taka wata rawa a zamantakewar su. Muna dauke da karin haske a cikin wanda ni Mohammad Nasiru Awal zan gabatar.

Madalla. Damir Mujagic dan shekaru 25 kyakkyawan misali ne na al´umomi daban daban a Bosniya. Mahaifinsa musulmi ne sannan mahaifiyarsa kuma ´yar Katholika ce mai asali daga wani iyali na Sabiya da Kuratiya. A lokacin yakin Bosniya Mujagic ya yi zama na wasu ´yan shekaru a nan Jamus. Ko da yake Mujagic dalibi a fannin koyon shirya fim, bai a reno na wani addini ba, amma ya karbi addinin Islama sanda yake dan saurayi. Kuma ko da yake matarsa wato Aida, musulma ce amma ya ce addini bai taka wata rawa ba lokacin da yake neman matar aure.

“Ba dole ba ne wai don sunan mace Hatica ko kuma don ta na musulma shi ke nan ta zama fitatta ta fi ko wace mace hali na gari ba, ko kuma wai don sunan mace Tanja ko kuma don ta zama ´yar Sabiya shi ke nan ta zama muguwar mace ba. A gaskiya ina kyamar masu nuna irin wannan bambamcin.”

Damir Mujagic da matarsa suna da guda daya. Ya ce zasu ba dan nasu tarbiya ta gari kuma idan ya girma ba zasu yi masa shisshigi dangane da matar da zai aura ba ko musulma ko kirista. To sai dai Mujadic ya ki ya ce uffan ko wannan matsayin zai dauka ga ´ya mace.

“Ko shakka babu zan samu matsala akan haka. Amma da mamaki domin ni ina mai ra´ayin cewa dukkan dan Adam darajarsa guda ce wato ba na fifita wani kan wani. Idan ina da ´ya sannan ta kawo wani mai bin wani addini daban ta ce zata aure shi, to a gaskiya za´a yi rikici. Domin dokokin addinin musulunci sun hana mace musulma ta auri namiji wanda ba musulmi ba. Haka shari´ar musulunci ta ce kuma ba zan so a karya dokokin addinin ba.”

Har zuwa wannan lokaci da ake ciki akwai tsofaffin alamun kasancewar addinai daban daban a birnin Sarajevo, to sai dai a halin da ake ciki musulmi sun fi kirista yawa. Safiye Schehovitsch jami´a a ofishin rajistar mazauna gari dake a cikin tsohon birnin Sarajevo ta tabbatar da cewa yanzu musulmi sun fi kowace al´uma yawa kuma ana yawan samun aurayya tsakanin su fiye da tsakanin sauran mazauna wannan birni.

“Tsarin mazauna wannan birni ya canza. Yanzu auratayya tsakanin kabilu da mabiya addinai daban daban ta ragu kamar a da ba. A bara alal misali daga cikin aure 296 da muka daura a wannan ofishin, hudu ko biyar ne kadai aka daura tsakanin masu bambamcin addini ko kabila.”

Gabanin yakin Bosniya yawan irin wannan auratayya ya kai kashi 30 cikin 100. To amma abubuwa sun canza inda yanzu kimanin kashi 60 cikin 100 na mazauna Bosniya ke nuna adawa da irin wannan aure.

Ga Yelena da saurayinta Nedim bambamcin addini ko kabila ba ya taka rawa a cikin zaman su. Yelena ´yar jarida ce mai jinin Sabiya da Kuratiya sannan saurayin na ta kuma musulmi ne da ke aiki da wannan kamfanin sadarwa. Nedim ya yi nuni da cewa matsayin addini ya canza tun bayan yakin a Bosniya.

“Yanzu mutane da yawa na bin dokokin addini. Da akwai wasu mutanen wadanda gabanin yakin ba su da cikakkiyar masaniya dangane da addinin Islama, amma yanzu sun san kabli da ba´adi na wannan addini kuma suna aiki da shi. Duk wadannan saboda yakin ne, wanda yanzu haka ya sa kowa ya dau damarar kare addinin sa.”

Da yawa daga cikin ´yan Bosniya kamar Nedim suna bin diddigin wannan yanayi na karkata ga addinin Islama, suna masu cewa ba al´adar Bosniya ba ne. Hakazalika suna kuma saka ayar tambaya ga aikin gina sabon babban masallaci wanda kasar Saudiya ke ba da kudin gina shi. A wani lokaci nan gaba kadan Yelena da Nedim ke shirin yin aure. Suka ce ba sa tunanin suna ko tarbiya ta addini da zasu ba ´ya´yansu.

“Bamu yanke shawara akan wani suna ba, amma ba zai yi nuni da wani addini ba. Zamu dauki matsayi irin na ´yan ba ruwan mu. Muna gudanar da dukkan bukukuwa kirmatti da da sauran bukukuwa na addinai daban daban.”

Ita budurwar ta sa Yelena ta yi karin bayani tana mai cewa.

“Ina gani kamata yayi a kyale yara su koyi addini kamar yadda al´uma su ke ganin sa. Dole ne su koyi ainihin abubuwan da suke a zahiri amma ina gani ba dole ne su bi wani addini ba.”