1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zamu taikamawa Iran idan aka kai mata hari-Al Sadr

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvB4

Babban malamin ´yan shi´a mai ra´ayin rikau a Iraqi, Muqtada al-Sadr ya ce baradan sa na Mahdi zasu taimaka wajen kare Iran, idan wata kasa ta kai mata hari. Al-Sadr wanda ke magana a gun wani taro da mai yin sulhu na Iran a shirinta na nukiliya Ali Larijani, ya ce an kafa wannan kungiya ce musamman don ta kare addinin Islama. Wannan jawabi na Al-Sadr ya biyo bayan furucin da shugaba Jacques Chirac na Faransa ya yi ne a tsakiyar makon jiya inda ya ce kasarsa ka iya zaban yin amfani da makaman nukiliya don mayar da martani na wani harin ´yan ta´adda.