1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a ƙasar Taiwan

June 26, 2010

Kimanin mutane dubu ɗari ne suka gudanar da zanga zangar nuna adawa da wata yarjejeniya da ƙasar Taiwan za ta rataɓa hannu akai tsakanita da ƙasar China

https://p.dw.com/p/O46F
Masu zanga zanga a ƙasar TaiwanHoto: AP

Dubai jama'a sun gudanar da zanga zanga a birnin Taipei na ƙasar Taiwan, domin yin Allah wadai akan shirin saka hannu da gwamnatin ƙasar ta ke shirin yi akan wata yarjejeniya cinikaya tsakaninta da ƙasar China.

Masu zanga zangar wanda yawansu ya kai dubu ɗari sun riƙa rera kallamun na yin suka ga hulɗar ta kasuwanci da aka shirya ƙasashen biyu zasu rataɓa hannu a rana talata mai zuwa, wacce kuma suke gani wani mataki na kai ga cimma nassara hadewar ƙasashen biyu

ƙasahen Taiwan da China dai sun kasance da gwamnatoci biyu daban daban tun a shekara ta 1949 bayan yaƙin bassasar da suka yi ,to amma haryanzu ƙasar China na ɗaukar Tsibirin na Taiwan da cewa wani yankinta ne .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita :Zainab Mohammed Abubakar