1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Brussels a game da rikicin Darfur

January 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuTr

Ɗaruruwan mutane, a birnin Brussels na ƙasar Belgium sun shirya zanga a yau lahadi, domin jawo hankalin al´ummomin dunia a game da ta´adin da ke wakana a yankin Darfur na kasar Sudan.

Alain Destexhe ɗan majalisar wakilai a Belgium, da ke ɗaya daga wanda su ka tsara wannan tafiyar jerin gwano, zuwa cibiyar ƙungiyar gamaya turai, ya ce sun yi hakan,da zumar yin hanun ka mai sanda, ga hukumomin EU.

Wannann zanga-zanga ta wakana a daidai lokacinda Ƙungiyar tawayen JEM, dake yankin Darfur, ta zargi sojojin gwamnati, ta yi mata luggudan wuta, tare da hallaka fara hulla 17, wanda ba su ci kasuwa ba, rufa ta faɗa kan su.

A cewar shugaban rundunar tawayen,Khalil Ibrahim, a duk tsawan ranekun juma´a da assabar, dakarun gwamnatin Kahrtum, sun yi ta shawagi, da jiragen sama a sararin samaniyar Darfur , su ka kuma cilla bama-bamai, da burin hana taron da ƙungiyoyin tawaye su ka tsara, da burin samar da haɗin kai kamin haɗuwa da tawagar gwamnati.