1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a habasha ta dauki sabon salo

November 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvMe

Daga can kasar habasha kuwa bayanai sun shaidar da cewa mutum biyu sun rasa ransu wasu kuma da dama sun jikkata. Hakan kuwa ya samo asali ne a sakamakon wata arangama data wanzu a tsakanin jamian tsaro da wasu masu zanga zanga a birnin addis Ababa.

Wannan arangama dai tazo ne kwanaki daya bayan jamian tsaron kasar sunn harbe mutane 23 daga cikin masu zanga zangar. Masu zanga zangar dai na nuna rashin amincewar su ne da sakamakon zaben daya bawa jamiyya mai mulkin kasar nasara, a zaben da aka gudanar a watan mayu na wannan shekara da muke ciki.

Daga dai lokacin da aka fara wannan zanga zanga izuwa yanzu an kiyasta cewa mutane 23 ne suka rasa rayukan su wasu kuma 150 suka jikkata.