1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Irak

April 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuO0

Ɗaruruwan dubban al´ummomin ƙasar Irak ke nan, a yayin da su ka shirya wata gagaramar zanga-zanga bisa gayyatar shugaban ɗarikar Schia´a Moqtada Sadr.

Wannan Zanga-zangar ta yi daidai da cikwan shekaru 4, da kiffar da gwamnatin tsofan shugaban ƙasa, mirganyi Saddam Hussain.

A biranen Bassorah, Kufa, Nadjaf da dai saura su, al´ummar ƙasar Irak, sun yi ta rera kalamomin tofin Allah tsine, ga ƙasar Amurika, da abokan ƙawance ta, a game da mamayen da su ke ci gaba da yi, ta hanyar laɓewa bayan wanzar da zaman lahia.

Wanda su ka shirya wannan zanga-zanga, sun buga ɗimbin takardu, ɗauke da bukatar dakarun Amurika su tattara yanasu-yanasu, su fice daga ƙasar Irak.

A yayin da ya kiri taron manema labarai albarkacin wannan rana, wani kakakin rundunar Amurika a ƙasar Irak, Amiral Mark Fox, ya bayyana baƙin ciki, da takaicin da ke tare da sojojin Amurika,ta la´akari da yadda wankin hulla ya kai su dare a ƙasar.

Kazalika, ya bayyana halin ƙunci, da sojojin Amurika ke ciki, a sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake babu ƙaƙƙabtawa, wanda ya zuwa yanzu, su ka yi sanadiyar mutuwar dakarun Amurika, kusan dubu 3 da ɗari 5.