1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Mozambik

September 1, 2010

Mutane shida sun rasa rayukansu yayin zanga-zanga a birnin Maputo na Mozambik.

https://p.dw.com/p/P1pk
Armando Guebuza, shugaban Mosambik.Hoto: picture alliance/landov

Aƙalla mutane shidda ne suka rasu, waɗanda suka haɗa da ƙananan yara biyu da kuma manyan huɗu a lokacin wata arangama tsakanin 'yan sanda da kuma masu zanga - zanga a sassa daban daban na Maputo, babban birnin ƙasar Mozambik a yau Laraba, kamar yadda majiyoyin 'yan sanda da na asibitoci suka shedar . Jami'an 'yan sanda sun bayyana yin amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma yin harbe - harbe da bindigogi, bayan da albarusan robansu ya ƙare wajen tarwatsa masu zanga - zangar, a yayin da suke ƙona tayoyi da kuma hana mutane zirga - zirga a wasu hanyoyi na babban birnin ƙasar ta Mozambique. Masu jerin gwanon sun ɗauki wannan matakin ne bayan da gwamnatin Mozambik ta yi shelar ƙarin kashi 30 cikin 100 na farashin Burodi a ƙasar. An dai kwatanta zanga - zangar a matsayin mafi muni da ƙasar, wadda ke fama da talauci ta fuskanta tun shekara ta 2008.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas