1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Siwaziland

September 8, 2010

Al´ummomin Siwaziland sun shirya zanga-zangar shimfiɗa demokraɗiya

https://p.dw.com/p/P7ED
Sarki Mswati III na Siwaziland na fuskantatar zanga-zangar shimfiɗa demokraɗiyaHoto: AP

 A wani mataki da gwagwarmayar shinfiɗa demokradiya, al´umar Ƙasar Siwaziland sun shirya zanga-zanga domin nuna adawar su da mulkin mulikiyar da ke gudana a ƙasar tun bayan da suka sami 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1968.

Masu fafatakar neman mulkin demokraɗiyya, sun gudanar da zanga-zangar ne a babban birnin ƙasar, wato Mbabane domin kawo ƙarshen tsarin mulkin sarautar galgajiya, wanda ƙasar Siwaziland kaɗai ke amfani da shi  a Nahiyar Afurka. Wannan zanga-zangar ta zo dai-dai da bukin tunawa da ranar samun 'yancin ƙasar yau shekaru 42 da suka wuce.

To sai dai Jami'an tsaron sun mamayi mutane 350 da suka halarci wurin kana suka yi awon gaba da shugaban Majalisar matasa Wandile Dludlu ba tare da sun bayyana laifin sa ba, wanda a dalilin haka ne sauran shugabanin ƙungiyoyin zanga-zangar suka dakatar da shirin su na miƙa sababbin manufofin su da takardar neman sauye-sauye zuwa ga hukumomin gwamnatin ƙasar.

Ana zargin Sarki Mswati na Siwaziland,da mulkin kama karya, saboda ya haramta kafa jamiyyu tun 1973.

 Mswati shi ke zaɓen frime minista da kuma mambobin majalisan dattawa da na dokoki. Kuma ana gudanar da zaɓe bayan kowani shekara biyar domin a tabbatar da yawan yan majalisun 

Daga bisani, yan sandan ƙasar sun kama a ƙalla mutun ukku daga cikin masu nuna adawan, bayan sun tsare mutane 50 dake taro a ranar jajibirin zanga-zangar. Zakhele Mabuza mai magana da yawun haramtaciyar jamiyyar adawa ta Peoples United Democratic Movement of Swaziland (PUDEMO) ya fada wa manema labarai cewa sun yi nasara a zanga-zangar farko saboda dama burin su, shi ne  hukumomin su san cewa daular ta Swaziland a yanzu mulkin demokraɗiya ta ke so.

Kimanin mutane dubu ɗaya ne suka fito ƙwan su da ƙwarƙwatan su a babban birnin na Manzini kafin su tafi babban birnin Mbabane, domin nuna goyon bayan su dangane da wannan ƙudurin na miƙa manufofin su zuwa ga gwamnatin ƙasar, domin a cewar su rashen demokraɗiyya ne ke kawo duk matsalolin da suke fuskanta a ƙasar.

Sarki Mswati III wanda ya gaji mahaifinsa Soubhuza II ya yi suna wajen irin ƙasaitaciyar rayuwar da ya ke yi da yawan aure-aure.

A duniya gaba ɗaya ƙasar Swaziland ta yi suna wajen yawan mutanen da ke fama da cutar SIDA, aƙalla mutun ɗaya a cikin kowani mutum huɗu na ɗauke da ƙwayar cutar.

Mawallafi: Pinado Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi