1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga kan tsadar abinci a Sudan

Salissou Boukari
January 16, 2018

Al'umma sun gudanar da wata kasaitacciyar zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan a wani mataki na nuna adawa da matsalar tsadar kayan masarufi.

https://p.dw.com/p/2qve8
Anti-Regierungsproteste im Sudan
Al'ummar kasar Sudan na zanga-zangaHoto: picture alliance/AP Photo

Masu zanga-zangar da suka hada da daliban jami'o'i da sauran al'umma na birnin Khartoum sun kasance masu nuna adawarsu tun farkon wannan wata kan yanayin hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a jihohi da dama na kasar.

Batu na baya-bayan nan shi ne na rubunya farashin biredi bayan wani mataki da gwamnatin kasar ta dauka na damka batun shigo da kayayyakin abinci ga wasu kamfanoni masu zaman kansu, wanda hakan ya haddasa bore a tsakanin al'ummar kasar ta Sudan.

Sai dai jami'an tsaro masu kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar tare kuma da kama masu zanga-zangar da dama cikinsu har da Siddig Yousse, wani kusa a jam'iyyar kwamunisanci ta kasar ta Sudan a cewar manema labarai da suka ganewa idanunsu lamarin.