1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga Zanga nuna ƙin jinin gwamnatin Israi'la a ƙasar Italiya

Sadissou YahouzaJune 4, 2010

Kimani mutane 2500 suka yi zanga zanga a birnin Rome domin yin Allah wadai da hare hare da sojojin Isra'ila su ka kai kan wani ayerin jirgin ruwa da ke kan hanyarsa ta zuwa Gaza.

https://p.dw.com/p/NiZW
Hoto: AP

Kimanin mutane dubu biyu da ɗari biyar ne suka gudanar da zanga zangar nuna ƙin jinin gwamnati Ira'ila a tsakiyar birnin Rome na ƙasar Italiya, domin yin Allah wadai da hare haren da sojojin ƙasar ta Isra'ila suka kai akan wani ayerin jirgin ruwan da ke ɗauƙe da kayan agaji zuwa zirin Gaza.

Mutane waɗanda suka riƙa ɗaga kwalayen a sa'ilin zanga zangar wanda ke cike da rubuce- rubuce na nuna ƙyamar Gwamnatin Isra'ilan ,sun yi kira da a kori Isra'ilan daga Majalisar Ɗinkin Duniya sannan kuma su gaggauta ficewa daga yankunan da suka mamaye na Palesɗinu.

Yanzu haka dai masu aiko da rahotanin sun ce wani sabon jirgin ruwan ɗauke da kayan agaji ƙarƙashin jagoranci wata ƙungiyar ta ƙasar Irlande, ya doshi yankin zirin Gaza ,kwanaki huɗu bayan harin na Isra'ila, wanda kuma gobe ake sa ran zai isa a Gazar

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Yahouza sadissou Madobi