1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangan karin farashin mai a Malasia

March 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7H

Malasia

Yansandan kwantar da tarzoma a na malasia sunyi amfani da ruwa da barkonon tsohuwa wajen watsar da gungun masu zanga zanga a birnin kuawa lumpur,adangane karin farashin mai.Ya zuwa yanzu dai an chafke mutane daga cikin masu gangamin.

Kimanin wakilan kungiyar kwadagon Malasian 300 suika gudanar da wannan zanga zanga na nuna adawa da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kara farashin mai,inda suka bukaci rage farashin cikin gaggawa.Duk dacewa yansandan kwantar da tarzoman sunyi amfani da barkonon tsohuwa da nufin tarwatsa masu boren,rahotanni daga birnin Kuala Lumpur na nuni dacewa,ana cigaba da wannan zanga zangar lumana,ayayinda wasu ke korafin cewa basu ga dalilin cafke mutane 7 da akayi ba.A watan daya gabata nedai gwamnatin kasar ta sanar da karin kudaden man petur da Diesel,da wajen kashi daya bisa biyar na ainihin farashin a baya.