1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-Zangar Adawa A Iraki

December 28, 2005

Tun misalin mako daya da ya wuce ake fama da zanga-zangar adawa da sakamakon zaben Iraki

https://p.dw.com/p/Bu2y
Zanga-zangar adawa da sakamakon zabe a Iraki
Zanga-zangar adawa da sakamakon zabe a IrakiHoto: AP

Hukum,ar zabe ta kasar Iraki ta ba da sanarwar cewa ta samu wasiku sama da dubu daya da dari biyar dake adawa da sakamakon zaben, ko da yake wasu ‚yan kalilan ne daga cikinsu ke da muhimmanci. Kungiyar Maraam ta hada har da jam’iyyar tsofon P/M Ijad Allawi da sauran kungiyoyi na ‚yan Sunna da kuma wasu jam’iyyun dake neman tabbatar da tsarin mulkin demokradiyya tsantsa a rikitacciyar kasar ta Iraki. Da yawa daga cikin kungiyoyi da jam’iyyun siyasar sun fara hangen wata alama ce ta asarar zaben dangane da sakamako na farko-farko da hukumar zaben ta gabatar, wanda a ganinsu ba shi akan wata sibga da gaskiya da adalci. Wannan shi ne dalilin da ya kai su ga hadin kai karkashin kungiyar da suka kira „Maraam“, wadda a yanzu ta tara kungiyoyi sama da 40 karkashin tutarta. A lokacin da yake bayani a game da manufar kungiyar, kakakinta Ali Tamimi cewa yayi:

Maraam ba kungiya ce ta addini ba, kamar yadda wasu ke ikirari, gamayya ce da ta kunshi kungiyoyi dabam-dabam wadanda suka shiga aka dama da su a shirye-shiryen zaben da aka gudanar bisa manufar ganin an cimma nasara domin kawo karshen rikice-rikicen dake addabar Iraki da samar da zaman lafiya ga al’umarta. Maraam kira take yi zuwa ga zaman lafiya.

Da yawa daga cikin ‚ya’yan kungiyar sun sake shiga zanga-zanga a birnin Bagadaza a jiya talata domin bayyana adawarsu da sakamakon zaben da aka ba da sanarwa kansa. A tsakanin masu zanga-zangar har da sakatare-janar na jam’iyyar ‚yan usulin Turkiyya Jamal Shand, wanda yayi bayani da cewar:

Dukkan jam’iyyun kabilar Turkawa sun hallara a wannan dandalin domin bayyana adawarsu da sakamako na karya da rashin adalci da aka bayar a game da zaben. Kiran da muke yi shi ne a kamanta adalci a tsakanin illahirin al’umar Iraki.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi kira a game da kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa da zai bi diddigin bukatun wasu jami’ai da jam’iyyun siyasar Irakin a wawware domin ta haka ne gaskiya zata yi halinta. Yau dai sama da mako guda ke nan ake fama da zanga-zanga a biranen kudanci da na tsakiyar Iraki. A bangare guda akwai masu neman ganin an gudanar da sabon zabe, sannan a daya bangaren kuma akwai masu neman ganin P/M Ibrahim Al-Jaafari ya ci gaba da rike mukaminsa. A kuma halin da ake ciki yanzu jami’an siyasa na gudanar da shawarwari domin neman bakin zaren warware wannan sabuwar matsala ta kasar Iraki ta samu kanta a ciki.