1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar adawa da sakamakon zabe a kasar Belarus

AbdullahiMarch 21, 2006

Yan adwar kasar Belarus sun kudiri aniyar cigaba da zanga zangar sai baba ta gani domin kawar da abin da suka kira gwamnatin mulkin kama karya

https://p.dw.com/p/Bu15
Masu zanga zanga a kasar Belarus
Masu zanga zanga a kasar BelarusHoto: AP

Daruruwan jamaár wadanda yawancin su matasa ne sun yi dandazo a dandalin Oktyabrskaya tare da dan takarar jamiár adawa Alexander Milinkevich inda suka yi kwanan zaune a wani abu dake zama koyi ga makamancin zanga zangar juyin juya hali na kasar Ukrain da aka yiwa lakabi da Orange revolution. Masu zanga zangar sun ce ko kusa ba zasu amince da sakamakon zaben da aka baiyana ba da suka ce an yi aringizon kuriú domin baiwa shugaban kasar mai ci Alexander Lukashenko nasarar sake yin tazarce a karo na uku a kan karagar mulki.

Zanga zangar wadda ta faro a ranar Lahadin da ta gabata, bayan kammala kada kuríar na kara samun goyon bayan jamaá inda madugun adawar ya yi kiran gudanar da gangamin kin amincewa da sakamkon zaben wanda ya baiwa shugaban kasar Alexander Lukashenko kashi 82.6 cikin dari na kuriún da aka kada, yayin da kuma dan takarar jamíyar adawar Alexander Milinkevich ya ke da kashi shida kacal na adadin kuriún. Rahotanni sun baiyana cewa mutane kimanin 10,000 ne suka halarci taron gangamin dake zama taron mafi girma a tsawon shekaru 12 da shugaban kasar Lukashenko ya yi yana mulkin kasar ta Belarus.

Masu zanga zangar wadanda suka bujirewa ruwan kankara da tsananin sanyi na dauke da tsohuwar tutar kasar mai launin fari da ja wanda Lukashenko ya sauya da kalar turar kasar Soviet, suna daukaka murya da cewa Allah ya taimaki kasar Belaru, kana sun kuma lashi takobin ba za su kau ba har sai an soke wannan sakamakon zabe don gudanar da wani zaben bisa gaskiya da adalci. A halin da ake ciki jamaá na ta kaiwa masu zanga zangar agajin abinci da abin sha a yayin da suka shiga rana ta biyu ta zangar zangar sai baba ta gani tare da kakkafa tantuna da rumfuna dake nuna cewa domin zaman dirsham har sai abin da hali yayi.

A waje guda kuma yan sanda na cigaba da yin sintiri suna hana kaiwa masu zanga zangar abinci. Sai dai kuma wasu na baiyana damuwa a dangane da barazanar da shugaban kasar yayi a makon da ya gabata na yin amfani sanya wando kafa daya da dukkan wadanda suka kudiri aniyar gudanar da wata zanga zanga. To amma masu zanga zangar sun ce kafa tantuna da kuma kwanan zaune da suka yi a dandalin wani gagarimin cigaba ne a kokarin jamaá na tabbatar da yancin su. Maáikatar harkokin wajen kasar Ukrain ta yi kira ga gwamnatin ta Belarus da kada ta ce za ta yi amfani da karfin tuwo a kan masu zanga zangar, ta na mai kira ga gwamnatin ta kare hakin alúmar tare da basu yancin yin zanga zanga cikin lumana. Yan adawar sun yi korafin cewa yan sanda sun kame magoya bayan su dama ciki kuwa har da wasu manyan jamiái hudu na madugun adawar Alexander Milikevich.

Shugaban kasar Belaru Alexander Lukashenko wanda ya shafe shekaru goma sha biyu yana mulkin kasar na fuskantar suka daga yan adawa da kuma kasashen yamma bisa gudanar da salon mulkin kama karya irin na taryyar Soviet.