1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da zaben Trump a Amurka

November 10, 2016

Gagarumar nasarar da Donald Trump ya samu a zaben shugaban kasa da ya gigita duniya a wannan larabar, ya jagoranci barkewar zanga zangar adawa a sassan Amurka.

https://p.dw.com/p/2SSJ6
USA Präsidentschaftswahl Protest gegen Donald Trump in San Francisco
Hoto: Reuters/S. Lam

A birnin New York dubban jama'a ne suka yi jerin gwano kan titi a yankunan Manhattan, suna cewar "shi ba shugaban kasata ba ne".

A birnin Chicago wajen mutane 1,000 ne suka yi kokarin yin cincirindo a kofar katafaren hotel din Trump da ke yankin.

An kiyasta cewar dalibai da malamai wajen 1,500 suka yi gangami a Berkely da ke California. Inda suka yi tattaki suna rera wakokin cewar "shi ba shugabanmu ba ne".

Rahotanni na nuni da cewar, a yayin da yawancin gangamin na Amurka ke gudana cikin lumana, a Oakland da Califonia, an yi ta jifan gine gine da kone-kone akan tituna. Amurkawan dai na kira da a sauya tsarin zaben kasar.