1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar adawa da ziyarar Paparoma a Turkiya

November 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuaA

Dubban jamaá sun yi dandazo a birnin Istanbul domin nuna adawa da ziyarar da Paparoma Benedict na XVI zai kai zuwa Turkiya a ranar Talata. ƙungiyar yan uwa musulmi wadda shugabannin ta suka nuna fushin su da kalaman da paparoman ya yi a watan Satumba inda ya danganta taáddanci da addinin Islama ita ce ta shirya gangamin. ƙungiyar ta ce saboda waɗannan kalamai na ɓatanci ga addinin musulunci bai kamata a kyale Paparoman ya kai tziyara ƙasar ba. Ziyarar ta paparoma zuwa Turkiya ita ce ta farko da zai kai zuwa wata ƙasa wadda ke da yawan musulmi a cikin ta.