1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar bore a Amurka ga dokoki da suka shafi baki

May 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buzt

Rahotanni daga Amurka na nuni da cewa dubbannin baki mazauna kasar sun shiga wani yajin aiki da nufin janyo hankalin mahukunta na sanin muhimmancin zaman su a kasar.

Matakin kauracewa shaguna da kuma makarantu na daga cikin mataki na baya bayan nan da baki mazauna kasar ta Amurka suka dauka na neman a gudanar da gyare gyare don bawa miliyoyin baki dake kasar izini na zama.

A dai watan disambar bara data gabata ne yan majalisar wakilai na kasar suka amince cewa shigowa Amurka ba tare da izini ba na daga cikin miyagun laifuka.

A can baya dai shugaba Bush ya tabbatar da cewa yana goyon bayan a bawa ire iren wadannan baki izini na zama, a matsayin ma´aikata, wanda hakan ka iya basu damar samun takardar izinin zama yan kasa a gaba.