1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar goyon bayan Darfur

September 17, 2006
https://p.dw.com/p/BujE

Masu zanga zanga suna ci gaba da yin gangami tare da taruka a bangarori da dama cikin duniya,suna masu bukatar a kawo karshen rikicin yankin darfur na kasar Sudan.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama sunyi kira ga gwanatin Sudan data amince da aikewa da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya zuwa yankin.

Rundunar zata maye gurbin dakarun kungiyar taraiyar Afrika ne,wadanda waadin aikinsu zai kare a karshen wannan wata.

Sudan har ya zuwa wannan lokaci taki amincewa da kasancewar dakarun majalisar Dinkin Duniya a yankin,tana mai cewa hakan zai zamanto sake yiwa kasar mulkin mallak ne.

Tun 2003,dubun dubatar mutane ne suka rasa rayukansu,fiye da miliyan 2 kuma suka tagaiyara cikin fada tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye da kuma sojin sa kai a yankin na Darfur.