1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar karin farashin man gas a Iraki

Zainab A MohammadDecember 19, 2005
https://p.dw.com/p/Bu7m

Dubban yan kasar Iraki ne ke wata zanga zanga ayau a birnin Bagadaza ,domin bayyana bacin ransu da karin farashin man gas da gwamnati ta aiwatar ,ayayinda ministan harkokin mai yayi barazanar yin murabus daga mukaminsa idan har baa dauki matakai na komar da farashin da ba.

Ayayinda mutane biyar suka gamu da ajalinsu kana wasu 11 suka jikkata daga hare hare acikin birnin bagadaza,Dakarun amurka sun sanar da sakin wasu manyan jamian gwamnatin Sadam hussein 8 dake tsare a kurkuku.

Yansanda dai nada harbi a Iska domin tarwartsa kimanin masu zanga zangan 3,000,wadanda ke jifa da duwatsu a kann tituna a garin Nasiriyah dake kudancin Irakin,wadanda kuma suka kaddamar da wannan gangamin tun bayan sanarwar gwamnati kann sabon farashin man a jiya lahadi.

Gwamnati dai tayi karin kashi 300 bisa 100 na farashin man gas,ayayinda jamiai a nasu bangare suka umurci gidajen sayer da mai dasu soke sabon farashin mai,domin kawo kwanciyar hankali.

A garin Amarah dake kudanci,masu gangamin sunyi ta jifan dakarun Britaniya da duwatsu,tare da waken Allah wadan manufofin Premier Ibrahim Jaafari.

A garuruwan Baquba da Tikrit kuwa,sai da jamian tsaro suka dauki tsauraran matakan tsaro a gidajen sayar da mai.

A dangane da cigaban tashe tashen hankulan nedai Minista kula da harkokin mai Ibrahim Bahr al-Ulum yayi barazanar ajiye mukaminsa,idan har gwamnatin Irakin bata soke wannan karin farashin na man gas ba.