1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar neman shugaba Bakiyev na Kirgistan da yayi murabus

November 3, 2006
https://p.dw.com/p/BudU
Dubban masu zanga-zanga a Bishek babban birnin Kirgistan sun ce zasu ci-gaba da yin gangami na neman shugaba Kurmanbek Bakiyev da yayi murabus. A jiya alhamis aka fara wannan zanga-zanga a tsakiyar birnin bayan da shugaba Bakiyev ya bijirema wani wa´adi na ya dauki wasu matakai da zasu rage masa karfin ikonsa. An rufe kantuna da kasuwanni bisa fargabar sake aukuwar mummunar zanga-zangar nan ta watan maris din shekara ta 2005, wadda ta tilasta tsohon shugaban kasar Askar Akayev sauka daga kan kujerar shugaban kasa. Yanzu haka an girke daruruwan ´yan sandan kwantar da tarzoma a kewayen fadar shugaban kasa. A yau ministan harkokin wajen Jamus ke sauka a birnin na Bishek inda zai tattauna da shugaba.