1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar Pakistan

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 16, 2006

Dubun dubatar masu kishin addinin islama na Pakistan ne suka kwarara cikin birnin Karachi a yau,a ci gaba da zanga zanga da akeyi a kasar ta Pakistan game da zanen batunci da akayiwa addinin islama.

https://p.dw.com/p/Bu1e
Hoto: AP

Masu zanga zanga kusan dubu 50,000 ne a yau suka cika birnin Karachi,suna masu kona mutum mutumi na shugaba Bush na Amurka da kuma na Firaministan Denmark Anders Fogh Ramussen.

Kodayake daga karshe dai masu zanga zangar sun watse lami lafiya,ba kamar yadda aka gudanar a biranen Islamabad da Lahore da kuma Pashewar ba a farkon wannan mako.

Daya daga cikin shugabannin wannan zanga zanga Mufti Muneeb Rahman,yayi kira ga Pakistan data katse dukkan hulda da kasashen turai,wadanda suka buga zanen zanen,tare kuma da kirawo jakadunta daga wadannan kasashe bayan ta kori jakadun kasashen daga cikinta.

An ji daga bakin wani dan tireda Mohammad Atik yana fadin cewa,idan har kasashen yammacin turai zasu marawa junansu baya,ta sake buga wadannan zane zane,to me zai hana gwamnatin Pakistan ta goyi bayan musulmi.

Yanzu haka dai inji wani babban jamiin tsaro na Pakistan,an tsare kusan mutane 350,cikin zanga zangar jiya laraba,wadanda suka hada da membobi da daliban kungiyar islama mafi tasiri ta Jamaat Islami.

Masu suka dai sunce batun yadda gwamnatin baya take anfani da kungiyoyin masu tsananin kishin addinin islama,ya sanya yanzu ake samu matsaloli wajen fuskantar duk wani abu daya shafe su.

Yanzu haka dai kungiyoyin islama na kasar Pakistan,sunyi kira da zanga zanga na gama gari a ranar 3 ga watan maris,a dai dai lokacinda ake sa ran,shugaban Amurka George Bush zai kai ziyara kasar ta Pakistan.

Shi kuma ana shi bangare,shugaba Parvez Musharraf daya daga cikin manyan abokan kawancen Amurka a yakinta da taaddanci,a jiya laraba ya kira wani taro inda yayi gargadi da kakkausar murya cewa,zai gwamnati zata shiga kafar wando daya da duk wanda ya nemi tada fitina.

Yanzu haka mutane akalla 3 suka rasa rayukansu ci kuwa har da wani dan shekaru 8 cikin zanga zanga daya barke a kasar tun ranar litinin.