1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar yan adawa a Belarussia

March 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv44

Dubun dubunan jama´a ne, masu goyan bayan jam´iyun adawa, su ka shirya zanga zanga yau ,a birnin Minsk na kasar Biolarussia, bisa gayyatar Alexandre Milinkevich, ɗan takara da sha kaye, a zaɓen shugaban ƙasa na ranar lahadi da ta wuce.

Tun farko makon da mu ke ciki, yan adawa su ka fara wannan zanga zanga, domin yin Allah wadai, ga tazarcen da shugaba Alexandre Lukachenko ya yi, a sakamakon wannan zaɓe.

A ranar jiya, jami´an tsaro,su ka tarwarsa,gungun masu tsatsawra ra´ayi , a wannan zanga zanga, da su ka shiga zaman durshin, na illah masha Allah, har sai lokacin da aka yi watsi da zaɓen.

A halin da ake ciki, ƙasashen turai da Amurika , sun bayyana goyan baya, ƙarara ga yan adawa , sun kuma haramta zaɓen shugaban ƙasar, da su ka ce, ya na cike da maguɗi, kazalika, sun yi Allah wadai, ga cin zarafin da shugaba Lukachenko ke wa yan dawa a wannan ƙasa.

Amurika da ƙungiyar gamayya turai, sun alkawarta haɗa ƙarfi, domin mayar da haramttatun hukumomin Minsk saniyar ware, kazalika, sun ƙudurci, aiki kafaɗa da kafaɗa har sai demokratiya ta bayyana a wannan ƙasa, da ke ɗaurin gidi Rasha.

Ministan harakokin wajen Belarussia, ya maida martini cikin fushi ga wannan ƙuduri na Amurika da tarraya Turai.