1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar yan adawa a Biolarussie

March 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4M

Duk da capke ɗaruruwan mutane da jami´an tsaro su ka yi, al´umma na ci gaba da shirya zanga a ƙasar Biolarussia, domin yin Allah wadai, da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da a ka gudanar ranar lahadi da ta wuce.

A sakamakon wannan zaɓe shugaba mai ci yanzu, Alexandre Lukachenko, ya yi tazarce, da fiye da kashi 82 bisa 100, na yawan ƙuriún da a ka shefa.

Yan adawa na zargin an tabka maguɗi ,da aringizon ƙuri´u.

A yanzu haka, dubunan mutane, a cikin sanhin hunturu, na zaman dirshin , a tsakiyar Minsk, babban birnin ƙasar, inda su ka ɗauri aniyar zama, har sai lokacin da gwamnati, ta yi watsi da sakamakon wannan haramtacen zaɓe.

Masu zanga zangar sun share kwanaki 2, a wannan dandali.

Su na buƙatar koyi, da abun da ya wakana a ƙasar Ukraine, a shekara ta 2004, inda jama´a, su ka ɗauri niyar, sai sun kiffar da gwamnati, su ka kuma samu nasara.

Ƙasashen EU sun yi Allah wadai, da maguɗin da ya wakana, a Biolarussia, saidai da dama, daga al´umma na kauttata zaton ƙasar Rasha, kaɗai ke da damar magance rikicin wannan ƙasa.