1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar yin tir da wariyar launin fata a Belgium

May 26, 2006
https://p.dw.com/p/Buwg

Dubun dubatan mutane a kasar Belgium sun gudanar da zanga-zangar yin tir da ayyukan nuna wariyar launin fata, bayan kisan da aka yiwa wata mace ´yar Afirka da yaron da take reno kimanin makonni biyu da suka wuce. ´Yan sanda sun ce mutane sama da dubu 20 suka shiga cikin zanga-zangar a birnin Antwerp dake arewacin kasar ta Belgium. Wani saurayi mai shekaru 18 wanda kuma ke da alaka da kungiyoyi masu matsanancin ra´ayin wariyar launin fata, ya halaka matar ´yar alalin kasar Mali da kuma yaron da take kula da shi. A wannan lokaci kuma saurayin ya jiwa wata ´yar Turkiya rauni. Birnin Antwerp dai ya kasance wani sansanin jam´iyar Vlaams Belang ta masu tsattsauran ra´ayin kyamar baki.