1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin ci zarafin yara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Abdourahamane HassaneApril 1, 2016

Ana zargin sojojin rundunar kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗikin Duniya MUNISCA da sojojin Faransa da laifin cin zarafin 'yan mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/1INin
Symbolbild französische Soldaten in Afrika
Hoto: PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images

MDD ta soma gudanar da wani sabon bincike a kan cin zarafin yara 'yan mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wanda ake zargin sojojin rundunar na Ƙasar Faransa watau Sangari da laifin aikatawa.A cikin wata sanarwa da wata ƙungiya mai zaman kanta da ke a birnin New York da ake kira da sunan Aids Free World ta bayyana,ta ce 'yan mata aƙalla guda 98 suka ba da shedun cewar tsakanin shekara ta 2013 zuwa wannan shekara.

Cewar sojojin rundunar na kiyaye zaman lafiya na MINUSCA na ƙasashen Gabon da Kwango da Burundi sun ci zarafinsu. Kana kuma suka ce daga cikin sojojin har'da wani na Ƙasar Faransa wanda ya riƙa tilasta wa 'yan mata yin jimai da karnuka