1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin sojan Jamus

October 5, 2006

Ana zargin Sojan Jamus da hannu wajen azabtar da wani Baturke haifaffen kasar a Afghanistan

https://p.dw.com/p/Btxr
Murat Kurnaz
Murat KurnazHoto: dpa - Bildfunk

Jim kadan bayan hare-haren sha daya ga watan satumban shekara ta 2001 Murat Kurnaz ya tashi daga birnin Bremen zuwa Pakistan. Manufar Kurnaz, wanda a wancan lokaci yake da shekaru 19 da haifuwa, shi ne ya shiga wata makaranta ta Alkur’ani. A pakistan aka cafke shi aka kuma danka shi a hannun sojan Amurka akan tsabar kudi dala dubu uku sannan aka tasa keyarsa zuwa Kandahar ta kasar Afghanistan. A can din ma sai da sojojin Amurka a hadin kai da wasu sojan Jamus su biyu suka rika azabtar da shi. Ga dai abin da lauyan Kurnaz ke cewa game da wannan kazamar ta’asa:

“An shimfide shi kasa aka daure masa hannuwa a baya, sannan daya daga cikin sojojin ya fizgo gashinsa ya daga kansa sama, ya kuma sake buga kan nasa da kasa. Bisa ga dukkan alamu don tsabar keta da kuma dadada wa Amurkawa rai, wadanda ke tsaye suna kallo.”

Sojojin na Jamus da aka tsugunar a Afghanistan lokacin yaki da Taliban , rukuni ne na bangaren kwantar da tarzoma da ake kiransu KSK a takaice. Wasu ‘yan kalilan daga hafsoshin sojan Jamus da jami’an siyasar kasar ne ke da masaniya a game da aikin wadannan sojojin a Afghanistan. A sakamakon haka ma’aikatar tsaro kan shiga kaka-nika-yi a duk lokacin da aka samu ire-iren wadannan rahotanni na ta’asa da rashin imani da sojojin na KSK ke aikatawa. An ji daga bakin ministan tsaro Franz-Josef Jung na mai ikirarin cewar wai kawo yanzu ba wani takamaiman bayanin dake nuna cewar sojojin Jamus sun azabtar da Kurnaz. A lokacin da yake magana da yawun ministan tsaron Thomas Raabe cewa yayi:

“Ma’aikatar tsaro zata nada wani kwamitin bincike, wanda zai bi bahasin zargin dalla-dalla. A matakin farko an bai wa dukkan sojojin da aka tura zuwa Kandahar a wancan lokaci umarnin gabatar da cikakkun bayanai a game da ayyukansu ba da wata-wata ba.”

To sai dai kuma a cikin hirar da mujallar Stern tayi da shi Murat Kurnaz dake da shekaru 24 a halin yanzu, ya sake fasa kwai, inda ya ce jami’an leken asirin Jamus sun sha fuskantarsa da tambayoyi a sansanin gwale-gwale na Guantanamo. Tuni kuwa gwamnati ta tabbatar da gaskiyar haka, inda ta ce an fuskance shi da tambayoyi har tsawon yini biyu a watan satumban shekara ta 2002. Amma Kurnaz ya ce an kuma sake fuskantarsa da tambayoyi a shekara ta 2004. Wani abin da ba tababa game da shi shi ne kasancewar tsofuwar gwamnatin Social-Democrats da the Greens sun ki amincewa da a sake maido da shi zuwa Jamus duk da tayin da Amurka tayi kafin sakinsa a cikin watan agustan da ya wuce. Dukkan wadannan batutuwan za a mayar da hankali kansu a karkashin wani kwamitin bin-bahasin na majalisar dokokin da za a nada a farkon shekara mai zuwa.