1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zeinab Diallo me kishin Fulani

MohaNovember 4, 2015

Zeinab Koumanthio Diallo mawakiya ce da ta dukufa wajen raya al'adun gargajiya Kabilarta da ke Guinea. Ta bude gidan kayan tarihi a garin Labé da ke zama mahaifarta.

https://p.dw.com/p/1GzPx
AoM Guinea Zeinab
Zeinab Koumanthio DialloHoto: DW

Zeinab Koumanthio Diallo mawakiya ce Bafullatana kuma ita ce shugabar gidan kayan tarihin kayan al'adun gargajiyar Fulani a Guinea. Shekaru 10 da suka wuce, bayan aiki a kungiyoyin kasa da kasa da rubuce-rubuce (“Les fous du 7ème ciel”) shi ne littafinta na baya bayan nan, ta koma yankinta na asali wato Futa Jallon, da ke tsakiyar kasar Guinea. Tun daga lokacin ta dukufa wajen raya al'adun gargajiyar Fulani makiyaya. Diallo ta gina gidan tarihi a Labé, inda ake baje kolin kayayyakin tarihin Fulani na yau da kullum. Yanzu haka an mayar da gidan tarihin wata cibiyar raya al'adun gargajiya. Zeinab Koumanthio Diallo ta kafa wata kungiyar makaranta littattafai a wani yunkurin shawo kan matasa su yi sha'awar al'adun gargajiya na Fulani.

Abubuwan rayuwar yau da kullum na da kyau ga gidan tarihi. Zeinab Koumanthio Diallo na rangadi a yankin tana ganawa da Fulani manoma game da kayayyakin tarihi.

"Ta adana kayayakin da ta gada daga iyaye da kakanne wanda zai yi kyau a gidan tarihinmu. Wannan kwarya ce da ake zuba madara ciki. Ana kiranta “birdugal” cikin Fulatanci. Mata na amfani da ita wajen tatsar nonon shanu.”

Adana al'adun gargajiya don yara manyan gobe: wannan shi ne aikin Madame Koumanthio. Shekaru 10 da suka wuce ta koma gida inda ta gina gidan tarhin.

AoM Guinea Zeinab
Diallo me kishin al'aduntaHoto: DW

“An gina al'dun gargajiyar Fulanin yankin Futa Djallon kan ginshikai guda uku: mata da shanu da kuma addini. Wannan ya nuna cewa al'adun Futa Djallon sun yi wa mata tanadi mai kyau”.

Taron kungiyar makaranta littattafai a gidan tarihin, ana karfafa gwiwar 'yan mata sun ba da ma'anar wasu tatsuniyoyi na tarihin Fulfulde da suka gada. Da haka suna samun kwarin gwiwa a cikin al'ummar da maza suka yi wa babakere.“Ina jin dadin karanta wakoki. Ina matukar son al'adunmu”.

Musulunci wani bangare ne na wannan al'ada. A shekarar 2011 Zeinab Koumanthio ta yi aikin Hajji a Makka sannan ta bude makarantar allo a garinta na Labé.

A nan ana nuna wa 'yan mata 'yancinsu ana kuma ba da muhimmanci kan rayuwa da kuma addini. Gidan tarihin na zama wata mahadar matasa, inda suke tabka mahawara da bayyana ra'ayinsu game da wasu al'adu cikin al'umma. Ramata Baldé, 'Yar Makaranta 'yar shekaru 14:

AoM Guinea Zeinab
Koumanthio Diallo da kayan koreHoto: DW

“An yi wa kawaye na biyu aure da wuri. Daya na da 13, dayar kuma 15. Ban ji dadin haka ba, amma ba abin da na iya yi. A nan 'yan mata ba su da 'yancin zaba wa kansu abin da suke so. Dole mu saurari iyayenmu. Yana da kyau ka ji maganarsu, amma wani lokaci ya kamata ka bijire."

Kamar wadannan matan, suna son su zama kafintoci su kuma dogara da kai. Zeinab Koumanthio Diallo, Shugabar Gidan tarihi ((Kulturbeauftragte in der Stadtverwaltung von Labé)).

“Ana ba wa 'yan matan nan horo mai kyau. Ba su yi koyi da kakannensu mata ba, wadanda suka ki koyon sana'o'i saboda mazajensu. Suna aiki kamar maza, sun kuma samu diploma."

A gidan Madame Koumathio abubuwa ba su canja sosai ba, har yanzu mata da 'yan mata ne ke kula da girke-girke.