1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabwe ta cika shekaru 27 da samun yancin kai.

April 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuNW

A kwana a tashi yau ne ƙasar Zimbabwe ke bikin cikwan shekaru 27, da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Britania.

Albarkacin wannan rana, shugaban Robert Mugabe, wanda ya jagorancin gwaggwarmar samun yancin kann, ya gabatar da wani zazzafan jawabi, inda yayi suka da kakkausar halshe, ga ƙasashen turai da Amurika, mussamman ga Praministan Engla Tony Blair, wanda Mugabe ke zargi da kitsa maƙarƙashiyar yi masa juyin mulki.

Wannan biki na wakana a daidai lokacin da ƙasar Zimbabwe ta tsunduma cikin rikicin siyasa, da kuma ƙuncin rayuwa, a dalili da tabarbarewa tattalin arziki da rashin aikin yi.

To saidai masu goyan bayan Shugaba Mugabe, da ke kan karagar mulki, tun samun yancin kan ƙasar, a shekara ta1980, na yaba masa, tare da jinjina masa dantse, a game da abunda su ka kira, jarimci, da kuma hazaƙar da ya nuna, ta fannin bunƙasa tattali arziki da kyauttata rayuwar jama´a.