1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabwe ta yi watsi da batun shigar Majalisar Ɗinkin Duniya cikin yunƙurin sasanta rikicinta na cikin gida.

May 25, 2006
https://p.dw.com/p/Buwt

Ƙasar Zimbabwe, ta yi watsi da shawarar bai wa Majalisar Ɗinkin Duniya damar shiga tsakani don warware rikicin siyasa da na tattalin arzikin da take huskanta a cikin gida. Jaridar nan Herald daily, mallakar gwamnatin ƙasar ce ta bayyana hakan, a cikin wani rahoton da ta buga a kan wannan batun, inda ta kuma ce gwamnatin shugaba Mugabe, ba ta miƙa wata sabuwar gayyata ga babban sakataren Majalisar Kofi Annan ya ziyarci ƙasar ba.

A jiya ne dai shugaban Afirka Ta Kudu, Thabo Mbeki, ya bayyana cewa, Majalisar Ɗinkin Duniya na tsara shirye-shiryen taimakawa, wajen kawo ƙarshen rikicin siyasa da na tattalin arzikin da ƙasar Zimbabwen ta daɗe tana fama da shi. A halin yanzu dai, rahotanni sun ce ƙasar, mai yawan al’umma miliyan 12, na huskantar matsaloli mafi muni a tarihinta, tun da ta sami ’yanci daga Birtaniya a shekarar 1980.