1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabwe tayi barazanar koran jakadu

March 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuPG

Gwamnatin Shugaba Robbert Mugabe na kasar Zimbabwe dake fama da adawa,ta gayyaci tare dayin barazanar koran dukkan jakadun kasashen yammaci na turai,wadanda ta ke zargi da yunkurin marawa yan adawa dake neman kifar da gwamnatin Mugabe baya.Ministan harkokin waje na kasar Sinbarashe Mumbengegwi ya fadawa gidan talabijin kasar cewa ,yayi gargadi wa jakadun kasashen na cewa,gwamnatin Mugabe bazata ji nauyin koran dukkan wanda ta kama yana hada kai da yan adawa domin kifar da gwamnatinsa ba.A hannu guda kuma yan adawa na cigaba da zage dantse wajen cimma burinsu na kifar da gwamnatin kasar kamar yadda wakiliyarsuTrudy Stevenson ta bayyana.