1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabwe tayi watsi da tayin da Afrika ta kudu ta bayar

Hauwa Abubakar AjejeMay 25, 2006

Kasar Zimbabwe tayi fatali da shawarar da kasar Afrika ta bayar na amincewa da Majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani domin kawo karshen rikicin siyasa da na tattalin arziki da ya ki ci yaki cinyewa a kasar dake kudancin Afrika

https://p.dw.com/p/Btzw
Hoto: dpa

Kafofin yada labari na Zimbabwe a yau sun ruwaito kakakin shugaba Robert Mugabe,wato,George Charamba na fadin cewa,batun shiga tsakani na majalisar dinkin duniya bata taso ba,inda yace babu shakka suna sane da cewa Amurka da Burtaniya suna kokarin sanya majalisar dinkin duniya cikin harkar kasar ta Zimbabwe,domin cimma wasu manufofinsu.

Shi dai shugaban kasar Afrika ta kudu,Thabo Mbeki ya nuna goyon bayansa ne ga ziyarar sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan,domin tattauna hanyoyin kawo karshen saniyar ware da kasashen duniya suka mayarda Zimbabwe da kuma fitar da ita daga cikin matasalar tattalin arziki da ta shiga.

Mbeki yace ya kamata kasashen duniya su sanya ido suga sakamakon shiga tsakani da Annan zaiyi maimakon mika shawarwarin kawo karshen rikicin kasar,wanda ya sanya mutane miliyan 12 na kasar suna fuskantar shiga cikin hali mafiya tsanani tun lokacinda suka samu yancin kai daga Burtaniya a 1980.

Akwai kuma rade raden cewa,Kofi Annan zai tattauna game da murabushin Mugabe bayan shekaru 26 yana mulki,a kasar da yanzu hauhawan farashin kayayiyaki ya haura kashi 1000 bida dari,daya daga cikin farashin masarufi mafiya kamari a duniya.

Kakakin na Mugabe ya kuma karyata cewa,gwamnati ta gaiyaci Annan zuwa kasar,yace abinda ya sani dai shine,gaiyatar da akayi masa bara,bayan Kofi Annan ya zargi gwamnati da rusa gidajen daruruwan jamaa,gaiyata da Charamba yace tuni ta tsufa.

Mugabe ya mikawa Annan gaiyata na ganewa idonsa abinda ya kira gyara da suka fara bayan rushe gidajen kimanin mutane dubu 700,gyara da masu suka suka ce yana tafiyar hawaniya.

Masu sukar aiyukan Mugabe suka ce maimakon gyaran,wannan shirin ya sake tsananta mawuyacin halinda tuni jamaar kasar suka shiga.

Shugaba Mugabe wanda yake kan karagar mulki tun 1980,ya wanke kansa daga zargin jefa kasar cikin halin da take ciki yanzu,yana mai zargin tsohuwar uwargijiyarsa Burtaniya da yin ja gaba wajen jan hankalin kasashen yammacin duniya suyiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa,saboda kwace gonakin fararen fata da yayi domin baiwa bakaken fata.

Kakakin Mugabe,yace sakamakon haka yanzu kasarsa tana karkashin haramtacen takunkumi,daga kungiyar taraiyar turai da Amurka saboda gyare gyare da tayiwa dokokinta na mallakar filaye.

Saboda haka a cewarsa wannan batu bai shafi majalisar dinkin duniya ba,batu ne tsakanin Zimbabwe da Burtaniya,abinda Zimbabwe take bukata inji shi,shine ya kamata majalisar dinkin duniya ta kalubalanci takunkumi da aka lakabawa kasar ta Zimbabwe.