1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zirayarar Steinmeier a kasashen tsakiyar Asiya

November 1, 2006
https://p.dw.com/p/Budn
Ministan harkokin wajen Jamus F-W. Steinmeier na ci-gaba da rangadin kasashen tsakiyar Asiya inda yanzu haka ya sauka a kasar Usbekitsan, mataki na biyu a wannan rangadi. An shirya ganawarsa da shugaban kasa Islam Karimov a birnin Tashkent, inda zasu mayar da hankali akan batutuwan kare hakin bil Adama. Bayan murkushe wata zanga-zanga a watan mayun bara, KTT ta sanyawa kasar takunkamai. A jiya ministan harkokin wajen na Jamus ya kai ziyara Kazakstan, inda ya tattauna da hukumin kasar akan burinsu na karbar shugabanci kungiyar tsaro da hadin kan Turai a shekara ta 2009. Mista Steinmeier ya danganta bawa kasar goyon baya idan aka samu wani ci-gaba na azo a gani akan sauye sauyen da take aiwatarwa.