1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Ahmadounedjad a Venezuela

September 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buj7

Shugaban ƙasar Iran, Mahamud Ahmadinedjad, ya kammala ziyara aikin da ya kai, a kasar Venezuela, inda ya gana da takwaran sa, Hugo Shavez.

A wani kakkausan jawabi da ya yi, a birnin Caracas, shugaba ya kaca kaca da gwamnatin Amurika da ya dangata da gwamnatin mulkin daniya da kama karya.

Ahmadounedjad, da mai masaukin sa, Hugo Shavez, na sahun gaba, daga masu adawa da manufofin Amurika.

Sun yi anfani da wannan dama, inda su ka ƙara jaddada aniyar su, ta sa kafar wando guda,da gwamnatin shugaba Georges Bush.

Ta fannin tattalin arziki, magabatan 2, sun cimma yarjeniniyar masanyar husa´o´i, a game da abunda ya shafi makamashi da haƙar man petur.

A game rikicin makaman nuklea,Iran ta samu goyan baya, a taron ƙasashe yan baruwa mu, da aka kammala ranar assabar a birnin Havana, na ƙasar Cuba.

Mahamud Ahmadinedhad, da Hugo Schavez, za su issa tare birnin New York, a taron shugabanin ƙasashen Majalisar Ɗinkin Dunia, inda su ka yanke shawara yin iya ƙoƙarin su, domin a gudanar da kwaskwarima, ga dokokin Majalisar.