1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Angela Merkel a ƙasar Amurika

Yahouza SadissouMay 4, 2006

Shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkell ta kammala ziyara aiki a ƙasar Amurika

https://p.dw.com/p/Bu0L
Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angeler merkell ta kammala ziyara aikin da ta kai a ƙasar Amurika, inda ta gana da shugaba Georges Bush.

Tawagogin 2, ,sun tantana batutuwa daban-daban da su ka jiɓanci harakoki diplomatia, tsakanin Jamus da Amerika.

Saidai batun rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran ya kasance a sahun farko na wannan haɗuwa.

Bayann mahaurori da masanyar ra´ayoyi sun cimma matsaya ɗaya a kan wajibcin warware wannan rikici ta hanyar diplomatia.

A yayin da ya ke jawabi ga yan jarida, George Bush ya ce ra´yin sa, ya zo daidai da na Angeller Merkel a game da hakan.

Ita ma a nata ɓangare Angeller Merkel, ta ce, ta na kauttata zaton, a samu bakin zaren warware wannan taƙƙadama cikin ruwan sanhi.

A dangane kuwa, da goyan baya, da Iran ke samu daga ƙasashen Rasha da China, Bush da Angeller Merkell, sun yi baki guda, a kan mahimancin samun ciwo kan, wannan ƙasashe.

A sakamakon wannan ziyara, Angeller Merkell, ta gayyaci Georges Bush, nan Jamus, a cikin watan Juli mai zuwa.

A wani gaman katari, ziyara ta yi daidai da ranar da ƙasashen Amurika, France da Britania, su ka gabatar wa

Komitin sulhu na Majlisar Ɗinkin Dunia, wani saban kundi mai ɗauke da buƙatar su, ta cilastawa hukumomin Teheran, watsi da matakin ƙera makaman nukleya. Wannan saban kundi, da har yanzu, Rasha da China ke adawa da shi, bai ambata ɗaukar matakan hukuncin ba ƙarara, saidai yayi barazanar binciken hanyoyin cilaswa Iran, bin umurnin wannan ƙasashe.

A fakaice, hakan na nufin,saka takunkumi kokuma, ɗaukar mattakan soja.

Ƙasashen 3, sun yi kira ga sauren ƙasashen dunia, da su kiyaye masanyar hussa´o´in kimiya, da Iran, domin hakan zai iya taimaka mata, ta cimma burin da ta sa gaba.

Sun bukaci komitin sulhu ya yi nazarin wannan saban kundi, kamin ranar litinin mai zuwa.

A nasa gefen ,wakilin ƙasar Rasha, a Majalisar Ɗinkin Dunia, ya sanar cewa, ƙasar sa, a shire ta ke ta bada haɗin kai, ga kundin, amma da sharaɗin a sake yi masa kwaskwarima.