1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Angela Merkel a Amirika

Yahouza Sadissou MadobiNovember 9, 2007
https://p.dw.com/p/C9qt

Nan gaba a yau ne, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, zata gana da shugaban ƙasar Amurika Georges Bush a gidan gonar sa, da ke Jihar Texas.

Ziyara ta Merkel a Amirika, na wakana kwanaki 2 bayan da shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy ya kammala ta sa.

Bush da Merkel za su tantana a kann batutuwa dabam-dabam, mussamman rikicin nuklear ƙasar Iran, da kuma halin da ake ciki a ƙasar Afghanistan.

A na fuskantar saɓanin ra´ayoyi tsakanin Amirika da Jamus, a game da wannan batutuwa.

Jamus ta bayyana adawa da manufar Amirika, ta yi anfani da karfin bindiga a kann Iran , sannan hukumomin Berlin hau kujera na ƙi, akan buƙatar Amirika ta ƙara yawan sojojin Jamus a Afghanistan.

A ɗaya wajen shugabanin 2, za su masanyar ra´ayoyi a game da rikicin ƙasashen Burma da Lebanon da dai sauran batutuwa da su ka shafi mu´amila a tsakanin su.